Pair of Vintage Old School Fru
+Labarai Da Rahotonni

An gwabza fada tsakanin 'yan Boko Haram

image

Rahotanni na cewa an yi arangama tsakanin bangarori biyu na kungiyar Boko Haram.


Rikicin dai ya samo asali ne tun bayan da kungiyar IS mai ikirarin kafa daular Musulunci ta sanar da Abu Mus'ab Al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar ta Boko Haram, wacce ta kira resehnta na yammacin Afirka.

Rashin jituwar ya kara ta'azzara ne a makonni biyu da suka gabata, lokacin da bangaren Al-Barnawi ya kai hari a kan mabiya Abubakar Shekau.

Kawo yanzu dai ba a iya tantance irin abin da rigimar tsakanin bangarorin kungiyar biyu ta haddasa ba sakamakon rashin kyawun hanyoyin sadarwa na zamani a arewa maso gabas.

Bambancin akida ne ya kawo rabuwar-kai a tsakanin bangarorin biyu.

Bangaren Al-Barnawi dai na zargin mabiya Abubakar Shekau da tsananta hare-hare a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Shi kuma Shekau yana zargin bangaren Al-Barnawi da cin amanar kungiyar.

Wasu dai na yi wa rigimar da ta dabaibaye Boko Haram kallon wata dama ga hukumomin tsaro su karasa murkushe 'ya'yan kungiyar.

Share Button

Kada ka karanta ka wuce ajiye ra'ayin ka game da An gwabza fada tsakanin 'yan Boko Haram
An wallafa a 2016-09-07 17:15
Alaka Boko Haram

Aika: F T G
Zama na farkon fadin ra'ayi game da An gwabza fada tsakanin 'yan Boko Haram
A Biyomu ta Facebook
Copyright © 2015 -
All Rights Reserved.