XtGem Forum catalog
+Labarai Da Rahotonni

Nigeria: Sule Lamido zai gurfana a gaban kotu

image

Wata majiya a rundunar 'yan sanda ta shiyya ta daya da ke Kano ta shaida wa gidan radio BBC cewa za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, a gaban kotu, ranar Talata.


Majiyar ta ce Sule Lamido zai bayyana ne a gaban kuliya a tsohuwar jihar da ya mulka wato Jigawa.

Gwamnatin jihar Jigawa ce dai ta kai koken cewa tsohon gwamnan ya yi kalaman tunzura mutane da ka iya janyo tashin-tashina.

A ranar Lahadi ne dai 'yan sanda suka kai samame gidan Sule Lamido da ke a birnin Kano.

Kuma a ranar ne suka gayyace shi domin bayani kan laifin da ake tuhumar sa da shi.

An dai ce Sule Lamido ya fada wa taron magoya baya cewa "su kasa, su tsare sannan su kuma raka akwatinan zabensu." a zaben kananan hukumomin da ke tafe a
jihar.

Wasu magoya bayan Sule Lamido dai na kallon kama tsohon gwamnan da yunkurin toshe bakin masu hamayya.

A baya dai shugaba Buhari ya sha amfani da irin wadannan kalamai a tarukan kamfe na neman zabensa.

Share Button

Kada ka karanta ka wuce ajiye ra'ayin ka game da Nigeria: Sule Lamido zai gurfana a gaban kotu
An wallafa a 2017-05-02 06:00
Alaka kotu , Nigeria , Sule Lamido

Aika: F T G
Ra'ayoyi game da Nigeria: Sule Lamido zai gurfana a gaban kotu
No Photo
haqq
2017-05-03 19:21

yayi kyau

A Biyomu ta Facebook
Copyright © 2015 -
All Rights Reserved.